ABNA24: Jonarhan ya ce ba aikin kungiyar ne sauke shugaban da aka zaba a wata a kasa ba, amma aikinta ne ta sasanta bangarorin da ke rikici domin a samu sulhu da zaman lafiya da kuma fahimtar juna.
Kungiyoyi da jam’iyyun siyasa da ke bore dai sun ki amince da shawarar da tawagar ECOWAS ta gabatar, da ke neman a kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar ta Mali, wadda za ta hada dukkanin bangarori.
A gobe Alhamis ne ake sa ran wata tawagar shugabannin kasashen yammacin Afirka, da ta hada shugabannin Nijar, Ghana, Ivory Coast da kuma Senegal za su isa kasar ta Mali, domin ci gaba da lalubo hanyoyin warware wanna rikici.
342/